Balotelli yana fuskantar tuhuma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Balotelli ya sauya rigarsa da Pepe ne duk da lallasa su da aka yi 3-0

Dan wasan Liverpool Mario Balotelli na fuskantar tuhuma daga wajen kocin kungiyar Brendan Rodgers bayan ya sauya riga da dan wasan Real Madrid, Pepe a wasan da suka sha kashi a gidansu da ci 3-0.

'Yan wasan biyu sun sauya rigarsu ne lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci, kuma an sauya Balotelli bayan dawowa hutun.

Rodgers ya ce, "ban amince da irin wannan sauya riga ba. Idan yana so ya yi hakan, ya kamata ya yi idan an kammala wasa. Don haka zan dauki matsayi a kan wannan batu ranar Alhamis."

Rodgers ya taba jin haushin dan wasa Mamadou Sakho lokacin da ya sauya rigarsa da ta Samuel Eto'o a Chelsea a kakar wasar da ta gabata.

Ya kara da cewa: "mun fuskanci irin wannan al'amari a kakar wasan da ta wuce kuma mun shawo kan lamarin a cikin gida."

Karin bayani