Nigeria ta fado mataki na 9 a iya taka leda a Afirka

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta kasa taka rawar gani a wasannin neman tikitin shiga kofin Afirka

Nigeria ta fado mataki na 42 a jerin kasahen da suka fi iya taka leda a duniya, kuma matsayi na tara a Afirk, a rahoton da hukumar FIFA ta fitar na watan Oktoba.

Nigeria dai tana mataki na shida a Afirka, kuma ta 37 a jerin kasashen da ke kan gaba wajen iya taka leda a watan Satumba da FIFA ta fitar.

Rahoton ya nuna cewa Nigeria ta samu koma baya ne sakamakon kasa taka rawar gani a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka.

Har yanzu Algeria ce ke mataki na daya a Afirka, Ivory Coast ta biyu, Tunisia a mataki na uku, Ghana A matsayi na biyar, Kamaru ta gusa zuwa mataki na 7.

Kasar Jamus ta ci gaba da rike matsayinta na daya a duniya, inda Argentina da Colombia su ma suke rike da matakinsu na biyu da na uku, yayin da Brazil ke mataki na biyar.

FIFA za ta fitar da jerin kasahen da ke kan gaba a jerin iya taka tamaula a duniya na watan Satumba ranar 27 ga watan.