Valdes zai yi atisaye da Manchester United

Victor Valdes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Valdes ba shi da kulob a yanzu, bayan da kwantiraginsa ya kare a bara

Tsohon golan Barcelona Victor Valdes zai yi atisaye a kulob din Manchester United a wani shirin da ya ke na murmurewa daga jinyar ciwon gwiwa da ya yi.

Dan kasar Spaniya, mai shekaru 32, ya ji raunin ne a cikin watan Maris, dalilin da yasa bai samu buga gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil ba.

United ta tabbatar da cewa Valdes zai yi atisaye kulob din, kuma likitocinta ne za su duba yadda ya ke samun sauki.

Kwantiragin Valdes ya kare a karshen kakar bara, bayan da dan kwallon ya ki ya amince ya tsawaita zamansa a Camp Nou.

Kocin United Louis van Gaal ya horas da Valdes a Barcelona a 2002-03, amma sai lokacin koci Radomir Antic golan ya samu damar kamawa Barca wasa akai-akai.