'Ban damu da rashin tsawaita kwantiragi na ba'

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Allardyce ya ce yana fatan West Ham za ta kare kakar bana cikin 'yan 10 farko

Koci Sam Allardyce ya ce bai damu da ba a tuntube shi ba, kan batun tsawaita kwantiraginsa da kulob din West Ham.

Allardyce wanda ya tsawaita zamansa da West Ham na tsawon tsekaru biyu a 2013, kwantiraginsa zai kare da kulob din a karshen kakar bana.

A bara magoya bayan kulob din sun yi ta kiraye-kirayen a sallami kocin, bayan da suka kare a mataki na 13 a teburin Premier, a bana suna matsayi na shida bayan wasanni takwas.

Allardyce, mai shekaru 60, ya ce a shekarunsa da ya yi a duniya, bai kamata yasa batun tsawaita zamansa a West Ham wani gagarumin batu ba.

West Ham ta dauko Allardyce a watan Yunin 2011, lokacin da kulob din ya fice daga gasar Premier.