Qatar: Za a bukaci Fifa ta sauya lokaci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption ECA ta ce ya fi dacewa a yi gasar lokacin damina

Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai za su bukaci Fifa ta yi gasar cin kofin duniya a Qatar a watan Mayu na shekarar 2022.

Gamayyar kungiyar kulob-kulob na Turai (ECA), wacce ta kunshi Manchester United, Liverpool, Barcelona da Bayern Munich, za su bukaci Fifa ta yi hakan ne saboda kaucewa yanayin zafi.

A shekarar 2010 ne dai Qatar ta yi nasarar karbar bakuncin gasar, sai dai an shafe fiye da shekara daya ana tattaunawa da zummar matsar da lokacin wasan daga lokacin zafi zuwa lokacin da yanayi zai inganta.

Ita dai ECA ta yi amanna cewa ya fi cancanta a yi gasar a lokacin damina.

Karin bayani