Real Madrid ta casa Bercelona 3-1

'Yan wasan real Madrid da Bercelona. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Madrid ta lallasa Bercelona ci 3-1

Kulob din Read Madrid ya casa Bercelona ci 3-1, a daya daga cikin wasanni mafiya daukar hankali a kwallon kafa.

Dole sai da kulob din Real Madrid da ke karbar bakuncin wasan ya zage dantse ya kwaci kansa bayan da aka zira masa kwallo a mintocin farko da fara wasan.

Neymar ne ya fara jefa kwallo a ragar 'yan Madrid minti hudu da shiga fili, kafin Ronaldo ya rama da bugun fanareti.

Minti biyar da dawowa daga hutun rabin lokaci sai Pepe ya jefa kwallo ta biyu a ragar Barca da ka bayan an dauko kwana.

Can kuma a minti na sittin sai Benzema ya sheka kwallo ta uku a ragar bakin da har yanzu su ne na daya a tebur da maki 22, yayin da Real Madrid take bi musu da maki 21 a wasanni tara.

Wasan mai suna El Clasico ya kunshi biyu daga cikin kungiyoyin da suka fi hada 'yan wasa masu matukar tsada a duniya.

A karon farko bayan shafe watanni hudu da dakatar da shi saboda cizon dan wasan Italia da ya yi, fitaccen dan wasan Uraguay Lius Suarez ya bayyana a cikin 'yan wasan Bercelona duk da cewar bai ci kwallo ko guda daya ba a wasan na yau.