Na ji dadin fara tamaula a Barca - Suarez

Louis Suarez Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Suarez ya ce Barcelona ba karamar kungiya ba ce ba

Luis Suarez ya ce ya ji dadi da ya fara buga wasan farko da Barcelona a karawar da Real Madrid ta doke su 3-1, bayan hukuncin dakatar da shi da aka yi watanni hudu.

Suarez mai shekaru 27, wanda ya koma Barcelona daga Liverpool kan kudi fam miliyan 75 a watan Yulin bana, shi ne ya bai wa Neymar kwallon da Barca ta fara cin Madrid.

Suarez ya ce "Na samu kwanciyar hankali da na dawo buga tamaula, kuma ban ji dadin rashin nasarar da muka yi ba".

Barcelona ta lashe wasannin La liga bakwai da ta buga lokacin da Suarez ke zaman hukunci, kuma wannan ne karon farko da aka doke ta a gasar.

'Yan jaridun Madrid suna ta rade-radin cewar Suarez ya kara teba, sakamakon rashin buga wasanni da ya yi, amma dan wasan ya ce yana kan ganiyarsa.