Manchester United da Chelsea sun tashi 1-1

Man United Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau biyu kenan Chelsea tana buga kunnen doki

Manchester United da tashi wasa kunnen doki da Chelsea a gasar Premier wasan mako na tara da suka buga ranar Lahadi.

Chelsea ce ta fara zura kwallo ta hannun Didier Drogba a minti na na takwas da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

United ta farke kwallonta ta hannun Robin van Persie daf a tashi wasa, bayan da golan Chelsea Thibaut Courtois ya tare kwallon da Marouane Fellaini ya kusa ci da kai.

Chelsea ta karasa wasa da yan kwallo 10, bayan da aka bai wa Branislav Ivanovic jan kati, kuma Southampton tana biye da Chelsea a matsayi na biyu da aka bata tazarar maki hudu.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi, Everton ta doke Burnley da ci 3-1 har gida, yayin da Tottenham ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da ci 2-1 har gida.