Kaduna United da Giwa sun tashi kunnen doki

NFF Logo
Image caption Saura wasanni biyu a kammala gasar Premier Nigeria

Kaduna United ta tashi wasa kunnen doki da Giwa Fc, a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 36, da aka buga a filaye daban daban dake fadin kasar ranar Lahadi.

El-Kanemi ta sha kashi a hannun Kano Pillars da ci 3-1, yayin da Nasarawa United ta doke Sunshine Stars da ci 2-1, sai Sharks da Warri Wolves suka tashi kunnen doki.

Karawa tsakanin Heartland da Taraba tashi wasa suka yi babu ci, Enyimba ta doke Nembe City har gida da ci 2-1, sai Gombe United da ta sa mu nasara akan Enugu Rangers da ci daya mai ban Haushi.

Saura wasanni biyu a kammala gasar Premier Nigeria, inda Kano Pillars ta ci gaba da zama a matsayi na daya da maki 62, sai Enyimba a mataki na biyu da maki 60.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Bayelsa United 3-1 Dolphin Crown FC 0-1 Abia Warriors El-Kanemi Warriors 1-3 Kano Pillars Gombe United 1-0 Enugu Rangers Heartland 0-0 Taraba FC Kaduna United 1-1 Giwa FC Lobi Stars 1-0 Akwa United Nasarawa United 2-1 Sunshine Stars Nembe City FC 1-2 Enyimba FC Sharks 1-1 Warri Wolves