Super Falcons sun lashe kofin Afirka

Asisat Oshoala Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria da Kamaru da Ivory Coast ne za su wakilci Afirka a Canada a badi

Tawagar kwallon kafar Nigeria ta mata ta lashe kofin nahiyar Afirka, bayan da ta doke Kamaru a wasan karshe da suka kara a Windhoek, Namibia ranar Asabar.

Falcons ta fara zura kwallon farko ta hannun Desire Oparanozie a minti na 12 da fara tamaula a bugun tazara, daga baya Asisat Oshoala ta kara ta biyu daf a tafi hutu.

Tun da aka fara gasar cin kofin Afirka ta mata, sau biyu ne kawai Nigeria ba ta lashe kofin ba, wanda Equatorial Guinea ta lashe a 2008 da 2012.

Nigeria da Kamaru sun sami gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Canada za ta karbi bakunci a badi, tare da Ivory Coast wadda ta doke Afirka ta Kudu da ci daya mai ban haushi a wasan neman matsayi na uku.