Chelsea ta nada Purslow matsayin shugaban tallarta

Christian Purslow Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ke matsayi na daya a teburin Premier

Kungiyar Chelsea ta nada tsohon daraktan Liverpool Christian Purslow a matsayin sabon shugaban tallace-tallacenta nan take.

Purslow, mai shekaru 50, ya yi aiki da Liverpool na tsawon watanni 16 kafin ya bar aikin a shekarar 2010.

Chelsea ta sanar a shafinta na Intanet ce wa "Tana shirye-shiryen tallata kanta da nufin kara yin fice a harkar kwallon kafa a duniya".

"Kuma Mr Purslow ne zai iya zagorantar cimma burinmu, domin yana da hangen nesa da kwarewar da ta kamata".

A makon da ya gabata Ron Gourlay ya ajiye aikin babban jami'in kulob din, inda shugaba Bruce Buck da Marina Granovskaia suke gudanar da wasu daga cikin aiyukansa.