An dakatar da Zidane koci tsawon watanni uku

Zinedine Zidane Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ta ce Zidane yana da cikakkun takardun horad da kulob

An dakatar da Zinedine Zidane daga horad da 'yan wasa na tsawon watanni uku, bayan da aka same shi da jagorantar wata kungiya ba tare da samun cikakkun takardu ba.

Hukumar kwallon kafar Spaniya ce ta dakatar da Zidane, bayan da ya jagoranci kulob din 'yan wasan Real Madrid na biyu wato Real Madrid Castilla.

Shi ma wanda ya yi wa Zidane mataimaki Santiago Sanchez an dakatar da shi watanni uku.

Real Madrid ta sanar a shafinta na Intanet cewa "Ba ta amince da hukuncin ba, kuma za ta daukaka kara har sai inda karfinta ya kare".

Ta kuma kara da cewa "Hukumar kwallon kafar Faransa ce ta ba shi izinin horas da matasan Madrid, abin da yasa suka ba shi kulob din".

Madrid ta nada Zidane sabon kocin 'yan wasa Madrid na biyu, bayan da ya yi aiki da Carlo Ancelotti a bara, wanda Real ta lashe kofin Zakarun Turai.