Bertrand ya zabi ya zauna a Southampton

Ryan Bertrand Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya ce ya ji daga wasa a Southampton a bana

Dan kwallon Chelsea Ryan Bertrand dake wasa a Southampton aro ya ce ya fara tattaunawa da kulob din domin ci gaba da buga mata tamaula.

Dan wasan mai tsaron baya, ya koma Chelsea ne ranar 30 ga watan Yuli, kuma karo na bakwai kenan yana barin Stamford Bridge zuwa wani kulob din wasa aro.

Betrand, ya buga wa Ingila wasanni biyu, kuma yana taka rawa a Southampton da kulob din yanzu yake matsayi na biyu a teburin Premier.

Ya kuma koma Chelsea daga Gillingham a shekarar 2005, daga baya aka ba da shi aro ga Bournemouth da Oldham Athletic da Norwich City da Reading da Nottingham Forest da kuma Aston Villa.