Chelsea ta doke Shrewsbury 2-1 a League Cup

Shrewsbury Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ke matsayi na daya a teburin Premier bana

Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar League Cup, bayan da ta doke Shrewsbury da ci 2-1 har gida a fafatawar da suka yi ranar Talata.

Chelsea ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Didier Drogba a minti na uku da dawo wa daga hutun rabin lokaci, kafin Shrewsbury ta farke kwallo ta hannun Andy Mangan mintuna 13 da ya shiga wasa.

Chelsea ta kara kwallo ta biyu da ya ba ta damar zuwa wasan daf da na kusa da karshe bayan da Jermaine Grandison ya ci gida daga kwallon da Williams ya bugo.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Bournemouth 2 - 1 West Brom MK Dons 1 - 2 Sheff Utd Shrewsbury 1 - 2 Chelsea Fulham 2 - 5 Derby Liverpool 2 - 1 Swansea