Ronaldo ne gwarzon dan wasa a Spaniya

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karon farko da Ronaldo ya zama gwarzon dan wasa a Spaniya

Dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo a karon farko ya zamo gwarzon dan wasa a gasar La Liga Spaniya na bana.

Wannan ne karon farko da Ronaldo, mai shekaru 29, ya lashe kyautar, bayan da ya doke dan kwallon Barcelona Lionel Messi.

Haka kuma dan wasan ya lashe kyautar wanda yafi yawan zura kwallaye a raga, da cin kwallon da tafi kayatarwa, a karawar da ya ci Valencia da dunduniya.

Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Spaniya a dai-dai lokacin da aka bayyana sunansa a cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon da yafi fice a duniya, wato Ballon d'Or.

Lionel Messi wanda shi ma yake cikin 'yan takarar Ballon d'Or ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi fice a Spaniya tun lokacin da aka kirkiro kyautar a shekarar 2008-09.

'Yan wasan Real Madrid ne suka fi yawa a lashe kyautukan da aka bayar a bana, inda Sergio Ramos aka zaba a mai tsaron baya da yafi fice, Luka Modric ya zama dan wasan baya mai buga tsakiya da yafi kwazo a gasar.