Ban gamsu da rawar 'yan wasa na ba - Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da karshe a League Cup

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce 'yan wasansa ba su burge shi ba a wasan League Cup da suka doke Shrewsbury da ci 2-1 ranar Talata.

Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da karshe da kyar, wanda sai da aka kusa tashi abokiyar karawar ta ta ci gida.

Mourinho ya ce "Na dauka 'yan wasan da basa buga tamaula akai-akai za su nuna kansu domin ayi gogayya da su, kuma na dauki tsawon lokaci kafin na fitar da 'yan wasan da suka buga karawar".

Kocin ya kuma yaba kwazon Didier Drogba da Oscar da Gary Cahill da kuma Filipe Luis kan buga wasan kwanaki biyu tsakani da suka buga da Manchester United.

Ya kuma ce yana da 'yan wasa kwararru da suka hada da Petr Cech da Mikel Obi da suka kware suka kuma so a fara wasan United tare da su.