Newcastle ta yi waje da Man City a League Cup

Man City Newcastle
Image caption Newcastle ta dawo da tagomashinta bayan da wasa ya juya mata baya

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ta doke Manchester City da ci 2-0 har gida a gasar League Cup da suka kara ranar Laraba.

Newcastle ta fara zura kwallon farko ta hannun Rolando Aarons kafin Moussa Sissoko ya kara kwallo ta biyu.

Wannan ne karon farko da Newcastle ta doke Manchester City a Etihad cikin wasanni 12 da suka fafata a filin.

Nasarar da Newcastle ta samu yasa ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar League Cup din.

Ranar Lahadi Manchester City za ta karbi bakuncin makwabciyarta Manchester United a gasar Premier wasan mako na 10.

Sauran sakamakon wasan da aka buga, Stoke ta sha kashi a hannun Southampton da ci 3-2, Tottenham ta doke Brighton da ci 2-0.