Swansea ta daukaka kara kan jan kati

Federico Fernandez Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Kocin Swansea na fatan FA za ta dage jan katin kafin su karawar da Everton

Kulob din Swansea ya daukaka kara kan jan katin da aka bai wa mai tsaron bayanta Federico Fernandez a karawar da Liverpool ta doke ta 2-1 a League Cup.

Fernandez, mai shekaru 25, an kore shi daga wasan ne nan take, bayan da ya yi wa dan kwallon Liverpool Philippe Coutinho keta mai muni.

Dan kwallon Argentina zai yi zaman hukuncin da ba zai buga wasanni uku ba, sakamakon laifin da ya aikata.

Swansea ta daukaka karar jan katin da alkalin wasa Keith Stroud ya bai wa Fernandez, kuma tana fatan za a yanke hukuncin da zai sa dan wasan ya buga karawar da za suyi da Everton ranar Asabar.