An rage hukuncin wasa babu 'yan kallo ga CSKA

CSKA Moscow Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption CSKA Moscow ce ta karshe a rukunin da Barcelona ke jagoranta

Hukumar kwallon kafar Nahiyar Turai UEFA ta rage hukuncin da ta yanke wa CSKA Moscow na buga wasa babu 'yan kallo, bayan ta daukaka kara.

Tun farko an dakatar da kulob din buga wasannin cin kofin Zakarun Turai guda uku babu 'yan kallo a gida, bayan samunta da laifuka da yawa, ciki har da kalamun wariya a fili.

Uefa ta mai da hukuncin zuwa buga wasanni biyu a gida babu magoya baya, wanda ta buga wasan farko da Manchester City har suka tashi 2-2.

Haka kuma UEFA ta rage yawan kudin da ta ci tarar kulob din daga fam 158,000, wanda yanzu za su biya fam 79,000.

Sai dai kuma CSKA ba za ta sayar da tikitin wasanninta biyu da za ta buga ga magoya baya ba, da kuma wanda za ta karbi bakuncin Roma ranar 25 ga watan Nuwamba da za su buga babu 'yan kallo