League Cup: Bournemouth za ta kara da Liverpool

Bournemouth Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karaon farko da Bournemouth za ta buga wasan daf da na karshe a League Cup

Kungiyar kwallon kafa ta Bournemouth za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan daf da na kusa da karshe a gasar League Cup.

Bournmouth wadda ta ke buga gasar Championship ba ta taba kai wa matakin wasan daf da na kusa da karshe a gasar ba, yayin da Liverpool ta dauki kofin karo takwas.

Sauran wasannin da za a buga Derby County za ta karbi bakuncin Chelsea, sai Sheffield United da za su fafata da Southampton.

Newcastle wadda ta doke Manchester City har gida, za ta ziyarci White Hart Lane domin karawa da Tottenham.

Za'a fara wasan daf da na karshe a gasar League Cup ne ranar 15 da watan Disamba.