Pellegrini na fargabar rashin kokarin kungiyarsa

Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ranar Lahadi ne Manchester City za ta karbi bakuncin Manchester United

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini na fargabar rashin kwazon 'yan wasansa a kwallo, yayin da za su kara da Manchester United a Premier ranar Lahadi.

Newcastle ta fitar da City wadda ta ke rike da kofin Premier a gasar League Cup, ta kuma tashi 2-2 a gasar cin kofin Zakarun Turai da CSK Moscow, sannan West Ham ta doke ta a gasar Premier.

Pellegrini ya ce "Yan wasanna ba su da yarda da aminci a tsakaninsu, kuma dole mu samu mafita kafin wasan mu da United".

Doke su 2-0 da Newcastle ta yi har gida a League Cup ya sa Pellegrini cikin shakku da kuma Manchester City cikin tararrabi.

City, wacce ta ke mataki na uku a teburin Premier za ta karbi bakunci United wadda ke matsayi na takwas a teburi da maki 13.