Na kware kan aiki na - Alan Pardew

Alan Pardew
Image caption Newcastle ta fara buga gasar Premier bana da kafar hagu.

Kocin Newcastle Alan Pardew ya ce ya kware kan horar da tamaula, bayan da suka doke Manchester City har gida a gasar League Cup ranar Laraba.

Pardew, mai shekaru 53, ya sha matsi daga magoya bayan kulob din bayan da suka fara gasar Premier bana da kafar hagu.

Sai dai kuma kulob din ya yunkuro, inda ya doke City da ci 2-0 a Ettihad a gasar League Cup da kuma doke Tottenham 2-1 a gasar Premier.

Newcastle tana matsayi na 14 a teburin Premier, kuma za ta kara da Tottenham a gasar League Cup wasan daf da na karshe ranar 15 ga watan Disamba.

Pardew ya jogoranci Newcastle kai wa mataki na biyar da na 16 da kuma matsayi na 10 a shekaru ukun da ya yi yana horar da kulob din.

Tuni magoya bayan kulob din suka janye kyallen dake dauke da sakon a kori Pardew wato 'sackpardew.com' da suka lika a filin wasa.