Chris Giwa ya janye kara kan zaben NFF

Chris Giwa
Image caption Fifa ta bai wa Nigeria wa'adin nan da Juma'a kan ta kawo karshen takaddamar NFF

Lauyan Chris Giwa da yake ikrarin cewa shi ne shugaban NFF ya sanar da cewa sun janye karar da suka shigar kotu, wadda ta rushe zaben Amaju Pinnick a matsayin shugaban kwallon kafar Nigeria NFF.

Wata kotu ce a Jos a makon jiya ta rushe zaben NFF da aka gudanar ranar 30 ga watan Satumba a Warri, inda Pinnick ya lashe zaben.

Kotun ta ci gaba da sauraren karar ranar Alhamis, wanda daga baya Giwa ya ce ya janye karar da ya shigar kan zaben NFF.

Hukumar kwallon kafar duniya FIFA ta bai wa Nigeria wa'adin sasantawa a NFF kafin Juma'a ko kuma ta dakatar da ita shiga harkar kwallon kafa.

Lauyan Giwa, Habila Ardzard ya ce sun janye karar ne saboda kiraye-kirayen da al'umma suka dunga yi domin samun ci gaban tamaula a Nigeria.

Shima Lauyan NFF, Joshuwa Ojoja ya ba da sanarwar janye karar da Giwa ya shigar bisa zaben shugaban hukumar kwallon Nigeria.

Sau biyu FIFA tana dakatar da Nigeria a wannan shekarar, ta kuma gargadi kasar da ta kawo karshen takaddamar NFF ko kuma ta fuskanci hukunci.