Raul ya koma kulob din New York Cosmos

Raul Gonzalez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Raul dan kasar Spaniya tsohon dan kwallon Real Madrid da Shalke da Al Saad ta Qatar

Tsohon dan kwallon Real Madrid da Schalke Raul, ya rattaba hannu a kwantiragin koma wa buga tamaula a kulob din New York Cosmos.

Raul, mai shekaru 37, ya amince da buga wa kulob din kwallo a farkon kakar badi, da kuma ba da sharawa ga matasan 'yan wasan kulob din na biyu.

New York Cosmos tana buga gasar kwallon kafa ta Arewacin Amurka NASL wacce ba ta kai gasar cin kofin Major League.

Raul, ya lashe kofin La Liga guda hudu da Spaniya Super Cup guda hudu da kuma kofin zakarun Turai uku da Real Madrid a shekaru 16 da ya yi a kulob din.

Ya kuma zura kwallaye 323 a wasanni 741 da ya buga wa Real, ya kafa tarihin yawan zura kwallaye a gasar Zakarun Turai inda ya zura kwallaye 71.

Ya buga wa Schalke wasa na tsawon shekaru biyu bayan ya bar Madrid a shekarar 2010, daga nan ya koma Al Sadd ta Qatar kafin ya yi ritaya.