An haramtawa Aleksandar buga wasanni bakwai

Aleksandar Tonev
Image caption Celtic ta ce za ta daukaka kara kan wannan hukunci

An dakatar da dan wasan Celtic Aleksandar Tonev buga wasanni bakwai saboda kalamai na wariyar launin fata da ya furta.

An aiwatar da wannan hukunci ne bayan da aka zargi Tonev da furta kalaman akan dan wasan Aberdeen Shay Logan a watan Satumba.

Sai dai hukumomin kungiyar ta Celtic sun ce za su daukaka kara akan wannan hukunci domin a cewarsu, dan wasan ba mai nuna wariyar launin fata ba ne.

Shi dai Tonev dan wasan aro ne daga kungiyar Aston Villa ta Premier league.