Bana son Steven Gerrard ya bar mu - Rodgers

Brenda Rodgers Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gerrard ya ce bai shirya yin ritaya ba, yana da sauran shekaru da zai ci gaba da taka leda

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce baya so kyaftin Steven Gerrard ya bar kulob din, bayan da ya ce zai iya barin Anfield idan ba a tsawaita kwantiraginsa ba.

Gerrard, mai shekaru 34, wanda daya daga cikin kashin bayan kulob din ne ya ce bai shirya yin ritaya ba, kuma zai iya komawa wata kungiyar domin ci gaba da taka leda.

Rodgers ya ce "Ya sanar da mai kula da wasan kyaftin din cewar suna bukatar ya ci gaba da wasa da kulob din, domin dawo da tagomashin kungiyar".

Kocin ya ce suna karacin mai zura kwallo a raga, bayan da aka tashi wasan da Newcastle ta doke su da ci daya mai ban haushi a St James Park.

Doke Liverpool da Newcastle ta yi yasa ta koma matsayi na bakwai da maki 14 a teburin Premier, bayan buga wasanni 10, kuma za ta ziyarci Real Madrid kafin ta kara da Chelsea.