An dakatar da Ferreira buga wasanni shekaru 50

Refree Red Card Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce hukuncin ya yi masa tsauri, domin yana sha'awar buga tamaula

An dakatar da Ricardo Ferreira mai buga kwallo a gasar cin kofin matasa na Switzerland daga buga wasanni na tsawon shekaru 50.

An hukunta dan wasan ne saboda samunsa da laifin buga wa alkalin wasa kwallo a fuska, sannan ya watsa masa ruwa tun daga kansa zuwa kasa.

Ferreira mai tsaron bayan kulob din Portugal Futebol, ya yi zaman hukuncin rashin buga wasanni 45, saboda samunsa da laifin cin zarafin abokan karawar su.

Dan wasan, mai shekaru 28 ya ce "Na dauka tsakanin shekara daya zuwa biyu za a hukuntani, amma shekaru 50 ai hukuncin nan ya yi tsauri".

Ferreira ya shiga wasan da suka buga da SC Worb a Bern League ne, bayan da aka dawo daga hutu, sannan ya ci zarafin alkalin wasa lokacin da ya kawo karshen wasa.

Dan kwallon zai gama hukunci ya kuma dawo buga tamaula ranar 5 ga watan Yuni 2064, lokacin kuma ya cika shekaru 78 da haihuwa.