NFF ta dawo da Stephen Keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stephen Keshi ne zai jagoranci Super Eagles a wasanni biyu na gaba

An sake maida Stephen Keshi a matsayin mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles, makonni biyu da hukumar NFF ta maye gurbinsa da Sha'aibu Amodu.

Keshi ya dawo kan mukaminsa ne bayan shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sa baki.

Najeriya za ta kara da Congo da Afrika ta Kudu a cikin watan Nuwamba, kuma tana bukatar lashe wasannin domin samun shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika a Morocco.

Shugaban NFF Amaju Pinnick da shugaban kwamitin kwararru na hukumar ta NFF Felix Anyansi-Agwu ne suka tabbatar da Stephen Keshi ne zai jagoranci wasannin biyu da suka rage.