Setif ta zama zakaran kofin kungiyoyin Afirka

Entente Setif Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasar Algeria ce ke matsayi na daya a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a Afirka

Kungiyar kwallon kafa ta Entente Setif ta Algeria ta lashe kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na Afirka, bayan da ta suka tashi 3-3 da AS Vita Club ta Jamhuriyar Congo.

Setif ta lashe kofin ne, bayan da suka tashi kunnen doki a karawar da suka yi a filin wasa na Mustapha Tchaker dake Blida, kwanaki shida bayan da suka buga 2-2 a Congo.

A karawa ta biyu da suka fafata ranar Asabar, AS Vita ce ta fara zura kwallo ta hannun Sofiane Younes minti hutu da dawowa daga hutu, kafin Lema Mabidi ya farke kwallo mintuna biyar tsakani.

Karo na biyu kenan da Setif tana doke kungiyoyi jamhuriyar Congo a shekarar bana, inda ta fara lashe TP Mazembe a wasan daf da na karshe.

Nasarar lashe kofin zakarun Afirka da Entente Setif ta yi, ya bata gurbin shiga gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyoyi da Morocco za ta karbi bakunci a badi.