Mourinho ya soki magoya bayan Stamford Bridge

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Mourinho ya ce sai anci kwallo za kaji muryar magoya bayan Stamford Bridge

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya soki magoya bayan kulob din a karawar da suka doke QPR 2-1 ranar Asabar da cewa sun yi shiru a Stamford Bridge kamar ba 'yan kallo.

Chelsea ta doke QPR a Stamford Bridge a gaban 'yan kallo 41,486, ta kuma ci gaba da rike matsayinta na daya a teburin Premier.

Mourinho ya ce "yanzu abu ne mai wahala su buga wasa a gida, saboda magoya bayanmu shiru suke yi, sai idan munci kwallo za kaji sowarsu".

A baya Mourinho ya soki salon 'yan wasansa da rashin kokari a gasar League Cup a fafatawar da suka doke Shrewsbury 2-1 ranar Talata.