Pillars ta lashe kofin Premier karo hudu

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Page
Image caption Karo na hudu kenan Pillars ta lashe kofin Premier Nigeria

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lashe kofin Premier karo na uku a jere, bayan da ta doke Nembe City da ci 4-0 a wasan mako na 37 da suka kara ranar Lahadi.

Nasarar da Pillars ta yi ya sa tana matsayinta na daya a teburin Premier da maki 65, kuma saura wasa daya ya rage a kammala gasar bana.

Kano Pillars ta lashe kofin Premier a shekarar 2007-08 da 2011-12 da 2013 da kuma bana, hakan na nufin kulob din zai wakilci Nigeria a gasar cin kofin zakarun Afirka a badi.

Kungiyoyin hudu ne ake sa ran za su fado daga buga gasar bana, yayin da tuni aka tabbatar da fadowar Kaduna United da Crown da kuma Nembe City.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Dolphins da Enyimba sun tashi wasa kunnen doki, yayin da karawa tsakanin Warri Wolves da Gombe United shi ma suka tashi wasa 1-1.

Kaduna United ta kwaso kwallaye hudu da nema a gidan Sunshine Stars, sai kuma Enugu Rangers da Nasarawa United da suka tashi canjaras, Giwa Fc ta doke Elkanemi 4-2.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Abia Warriors 3 vs 0 Sharks Akwa United 0 vs 1 Heartland Bayelsa United 4 vs 1 Lobi Stars Dolphin 1 vs 1 Enyimba FC Enugu Rangers 0 vs 0 Nasarawa United Giwa FC 4 vs 2 El-Kanemi Warriors Kano Pillars 4 vs 0 Nembe City FC Sunshine Stars 4 vs 0 Kaduna United Taraba FC 3 vs 0 Crown FC Warri Wolves 1 vs 1 Gombe United