Manchester City ta doke United da ci 1-0

Mancity Manunited
Image caption City tana matsayi na uku a teburin Premier bana

Manchester City ta doke Manchester United da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 10 da suka buga a Ettihad ranar Lahadi.

Sergio Aguero ne ya zura kwallon bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, kuma kwallo ta hudu kenan da ya ci United a Ettihad.

Golan United David De Gea sau biyu yana hana Aguero zura kwallo a raga, kafin a kori dan wasan United Chris Smalling daga wasan.

Shi ma golan City Joe Hart ya hana United ta zura masa kwallo a raga, musamman damar da Robin van Persie da Angel di Maria suka samu.

Nasarar da City ta samu yasa tana matsayi na uku a teburin Premier da tazarar maki shida tsakaninta da Chelsea wadda take mataki na daya.