Pardew na murnar dawo da tagomashin Newcastle

Alan Pardew Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kocin ya fada a baya cewar zai iya jure duk wani matsin da za ayi masa

Kocin Newcastle United Alan Pardew ya ce a shirye ya ke ya yi shawagi a tsakiyar birnin Newcastle, bayan da ya dawo da tagomashin kulob din a kakar bana.

Magoya bayan kulob din a baya sun yi ta kiraye-kirayen a kori Pardew daga kocin kulob din bayan da suka fara kakar bana da kafar dama.

Newcastle ta zamo ta karshe a teburin Premier, bayan da Southampton ta doke ta 4-0 a watan Satumaba.

Tun daga lokacin kulob din ya yunkura, inda ya lashe maki 11 daga cikin manyan wasannin da ya buga.

Newcastle ta doke Liverpool da ci daya mai ban haushi ranar Asabar a gasar Premier, hakan yasa ta lashe wasanni uku a jere kenan, ta kuma koma mataki na 11 a teburin Premier.

Haka kuma kulob din zai buga wasan daf da na kusa da karshe da Tottenham a gasar League Cup.