Sunderland ta doke Crystal Palace har gida 3-1.

Palace Sunderland Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sunderland ta kara yin sama a teburin Premier

Sunderland ta doke Crystal Palace a Selhurst Park da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka fafata ranar Litinin.

Fletcher ne ya fara zura kwallo a raga da kai a minti na 31 da fara tamaula, inda Palace ta farke kwallo ta hannun Wes Brown bayan da ya ci gida.

Sunderland ta kara kwallo ta biyu ta hannun Jordi Gomez, kafin a bai wa dan kwallon Palace Mile Jedinak jan kati a karawar.

Daf a tashi wasa Sunderland ta kara kwallo ta uku a raga ta hannun Fletcher, kuma nasarar da Sunderland ta yi yasa ta bar matsayin kungiyoyin da ka iya fadu wa daga gasar Premier