World Cup 2022: Ana tattaunawa kan lokacin fara wasa

Qatar 2022 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana ta takaddamar lokacin da ya kamata a fara gasar kofin duniya a 2022

Manyan masana kwallon kafa a duniya na tattaunawa a Zurich domin tsayar da ranar da ya kamata a fara Gasar cin Kofin Duniya a Qatar a shekarar 2022.

FIFA ta hakikance cewar ba zai wu a fara gunanar da wasannin cin kofin duniya tsakanin watan Yuni da Yuli ba, sakamakon yanayin zafi a shiyyar.

Manyan batutuwa biyar da za a gabatar a wurin taron sun hada da lokacin da ya kamata a fara gasar don kaucewa yanayin zafi.

Manyan masana kwallon kafa da ke halartar taron sun hada da babban jami'in gasar Premier Richard Scudamore da sakataren kwallon Birtaniya Alex Horne da shugaban tsare-tsaren karbar bakuncin gasar Hassan Al Thawadi da wakilan gasar wasannin kasashe da kuma na nahiyoyi.

Bayan kammala taron za a mika wa kwamitin amintattun FIFA batutuwan da aka tattauna domin yanke hukunci a watan Maris na badi.

Tun a baya an ba da shawar fara gasar ta 2022 tsakanin watan Nuwamba da Disamba.