Watakila Bale ya buga karawa da Liverpool

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale bai buga wasan farko da Madrid ta doke Liverpool 3-0 ba

Watakila dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ya buga wa kulob din karawar da zai yi da Liverpool a gasar kofin zakarun Turai ranar Talata.

Bale, mai shekaru 25, wanda ya koma Madrid daga Tottenham a watan Satumbar 2013, rabon da ya buga wa Real tamaula tun ranar 5 ga watan Oktoba.

Carlo Ancelotti ya ce "Ya warke daga raunin da ya ji, sai dai ban sani ba idan za a fara wasan da shi ko kuma ya shiga bayan an koma daga hutu".

Shi kuwa dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge da kyar ne idan zai iya buga wasan, amma kulob din ya tafi da shi filin wasa na Bernabeu.