Arsenal ta tashi wasa 3-3 da Anderlecht.

Arsenal Anderletch Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saura wasanni biyu ya rage su buga na cikin rukuni

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na daf da samun tikitin buga wasan zagayen gaba a gasar cin kofin zakarun Turai, duk da tashi wasa 3-3 da Anderlecht.

Mikel Arteta ne ya fara zura kwallon farko a dukan fenariti, bayan da Chancel Mbemba ya yiwa Danny Welbeck keta a cikin da 'ira ta 18.

Alexis Sanchez ne ya kara ta biyu a buga kwallon da ya yi daga yadi 20, kafin Alex Oxlade-Chamberlain ya kara ta uku a raga.

Anderletch ta fara farke kwallon farko ta hannun Anthony Vanden Borre da ta biyu da ya buga daga bugun fenarity, kafin su farke ta uku ta hannun Aleksandar Mitrovic.

Bayan buga wasanni hudu Borussia Dortmund ce a matsayi na daya da maki 12, sai Arsenal da maki 7 a mataki na biyu, RSC Anderlecht ta uku da maki 2, sai Galatasaray mai maki daya kacal.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

Juventus 3 - 2 Olympiakos Malmö FF 0 - 2 Atl Madrid FC Basel 4 - 0 Ludo Razgd Real Madrid 1 - 0 Liverpool Zenit St P 1 - 2 Bayer Levkn Benfica 1 - 0 Monaco Bor Dortmd 4 - 1 Galatasaray