Kulob din Real Madrid ne jagaba a duniya

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Liverpool tana matsayi na uku a rukuni na uku

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce kulob din Real Madrid ne wanda ya fi fice a duniya, amma ya ce kulob dinsa ma ba a baya yake ba wajen taka leda.

Liverpool, tana matsayi na uku a rukunin na biyu, wanda za ta kara da Real Madrid ranar Talata, kuma an zura mata kwallaye 21 daga wasanni 15 da ta buga a bana jumulla.

Rodgers ya ce "Kungiyata ta taka rawar gani a karawar farko da muka yi, masu tsaron bayan mu ne suka yi kurakuren da Madrid ta samu nasara a kanmu".

Liverpool wadda ta kare a matsayi na biyu a gasar Premier a bara, ta fara kakar wasan bana da kafar hagu, inda take mataki na bakwai bayan buga wasanni 10.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Liverpool a filin wasa na Bernebeu ranar Talata, inda ta doke Liverpool 3-0 a karawar farko da suka yi a Anfield.