Northern Ireland ta gayyato Paddy McNair

Paddy McNair Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karon farko da dan wasan zai fara buga wa kasarsa kwallo

Northern Ireland ta gayyato dan kwallon Manchester United Paddy McNair cikin tawagar 'yan wasanta, domin buga wasan neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Turai da Romania.

McNair, mai shekaru 19, shi ne sabon dan wasa daga cidan 'yan kwallo 25 da aka bayyana sunanyen wadanda aka gayyato ranar Talata.

Mai tsaron baya Aaron Hughes da mai zura kwallo a raga Jamie Ward suna cikin tawagar, duk da cewa suna jinyar rauni.

Sai dai kuma dan wasan United mai tsaron baya Jonny Evans ba ya cikin wadanda aka gayyato, sakamakon jinyar da yake yi har yanzu bai buga wa kasar wasa ba.

Northern Ireland za ta kara da Romania ranar 14 ga watan Nuwamba a Bucharest.

Ga sunayen 'yan wasa 25 da aka gayyato:

Masu tsaron raga: R Carroll (Notts County), A Mannus (St Johnstone), M McGovern (Hamilton Academical).

Masu tsaron baya: A Hughes (Brighton), C Baird (West Bromwich Albion), G McAuley (West Bromwich Albion), R McGivern (Port Vale), C Cathcart (Watford), C McLaughlin (Fleetwood Town), L McCullough (Doncaster Rovers), R McLaughlin (Liverpool), P McNair (Manchester United).

Masu wasan tsakiya: S Davis (Southampton), C Brunt (West Bromwich Albion), S Clingan (Kilmarnock), C Evans (Blackburn Rovers), O Norwood (Reading), B Reeves (MK Dons), P McCourt (Brighton), N McGinn (Aberdeen).

Masu zura kwallo: K Lafferty (Norwich City), J Ward (Derby County), J Magennis (Kilmarnock), B McKay (Inverness Caledonian Thistle), Will Grigg (MK Dons).