CSKA Moscow ta doke Manchester City da ci 2-1

Mancity CSKA Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man City ce ta karshe a rukuni na biyar da maki biyu kacal

Manchester City ta sha kashi a hannun CSKA Moscow da ci 2-1 har gida a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara ranar Laraba.

Seydou Doumbia ne ya fara zura kwallon farko a ragar City da kai, kafin Yaya Toure ya farke kwallon daga bugun tazara.

CSKA ta kara kwallonta na biyu ta hannun Doumbia a minti na 32, bayan da ya zari kwallo ya kuma dangana da raga.

City ta karasa karawar babu 'yan wasanta biyu, inda aka kori Fernandinho da Toure daga wasan.

Doki City da aka yi yasa ta koma mataki na karshe a rukuni na biyar da maki biyu, wanda Bayern Munich ce take matsayi na daya da maki 12, Roma a mataki na biyu da maki hudu, sai CSKA ta uku da maki 4.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Bayern Mun 2 - 0Roma

Ajax 0 - 2 Barcelona

Paris St G 1 - 0 Apoel Nic

NK Maribor 1 - 1 Chelsea

Sporting 4 - 2 Schalke

Ath Bilbao 0 - 2 FC Porto

Shakt Donsk 5 - 0 BATE Bor