A buga kofin duniya lokacin sanyi - Platini

Michel Platini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Platini ya ce babu lokacin da ya kamata a fara gasar da ya wuce lokacin Sanyi

Shugaban hukumar kwallon kafar nahiyar Turai, Michel Platini ya shaidawa BBC cewa ya kamata a buga gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karba bakunci a 2022 a lokacin sanyi.

Shawarar Platini ta yi hannun riga da wadda manyan kungiyoyin Turai suka bayar, inda suka bukaci a gudanar da gasar a watan Mayu.

Mahukuntan gasar Premier da La Liga da Bundesliga na hangen idan aka gudanar da gasar kofin duniya kamar yadda aka saba, to hakan zai kawo tsaiko ga wasanninsu.

Ana gudanar da wasannin cin kofin duniya ne tsakanin watan Yuni da Yuli, sai dai FIFA ta shaidawa Qatar cewa buga gasar a lokacin bazara zai jefa rayuwar 'yan wasa a cikin hatsari.