Matasan 'yan kwallon Afrika

Nan da kwanaki hudu za a sanarda sunayen 'yan kwallon Afrika da za su yi takarar neman kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na BBC a 2014. Ko da yake 'yan wasa biyar da aka kebe sun yi fice a nahiyar, amma kuma akwai wasu matasa masu hazaka da nan gaba za su iya haskakawa. Sashin wasanni na BBC ya zabo uku daga cikinsu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aurier ya kasance barazana ga Emmanuel Eboue

Serge Aurier Dan shekaru 21, Serge Aurier ya kasance son kowa a Faransa. An haife shi a Ouragahio na Ivory Coast, ya koma Faransa tare da iyayensa inda suka yada zango a Seine-Saint-Denis da ke arewacin Paris. Ya soma taka leda a karamar kungiyar mai suna FC Villepinte kafin ya koma RC Lens. Aurier yana dan shekaru 17 ya soma buga wa Lens a gasar Faransa a shekara ta 2009. Ya koma Toulouse a watan Junairun 2012 abinda ya ja hankalin Ivory Coast ta gayyace shi wasa. A watan Yunin 2013, Aurier ya bugawa Ivory Coast wasan farko tsakanin ta da Gambia abinda kuma yasa aka gayyace shi gasar cin kofin duniya a Brazil. Didier Drogba ya bayyana Aurier a matsayin "dan wasan baya a bangaren dama da ya fi kowa a Faransa." Bayan kamalla gasar cin kofin duniya Toulouse ta bada aronsa zuwa Paris St-Germain.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yi tare da Bentaleb sosai a Tottenham

Nabil Bentaleb Nabil Bentaleb ya soma kwallon kafa da kafar dama. Bayan ya bar kungiyar da ke mahaifarsa a Lille lokacin yana da shekaru 15, sai ya koma kungiyar Mouscron ta Belgium kafin ya koma Dunkerque a Faransa. Tsohon kocin Tottenham Harry Redknapp, ya gano Bentaleb a shekara ta 2012 inda daga nan ya kulla yarjejeniya da Spurs. Kwallonsa ta samu daukaka bayan da Tim Sherwood ya zama kocin Tottenham inda ya ba shi damar buga kwallon farko tsakaninsu da Southampton a watan Disambar 2013. Bentaleb wanda aka haifa a Faransa, ya zabi buga wa kasar iyayensa watau Algeria inda ya buga wasan farko tsakanin Desert Fox da Slovenia. A gasar cin kofin duniya Brazil, Bentaleb ya buga duka wasannin Algeria sannan sabon kocin Tottenham Mauricio Pochettino na wasa tare da shi so sai.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brahimi ya jiya wa Faransa baya

Yacine Brahimi Yacine Brahimi ya yi farin jini sosai a Faransa, inda shekara ta 2006, Paris Saint Germain ta yi zawarcinsa amma kuma sai iyayensa suka buka ce shi ya kulla yarjejeniya da Stade Rennais. Brahimi ya yi fama da rauni a kungiyar kuma ya samu rashin jituwa tsakaninsa da kocinsa Frederic Antonetti. Ya koma Granada a Spain abinda ya dawo masa da tagomashinsa. Bayan ya haskaka a gasar cin kofin duniya tare da Algeria, sai ya koma FC Porto a bazarar 2014. Cikin wasanni 11 a Portugal, Brahimi ya zura kwallaye hudu cikin wasanni 11. Ya haskaka tare da Algeria, inda ya zura kwallaye biyu a cikin wasannin share fage na neman cancantar buga gasar cin kofun nahiyar.