Vincent Kompany bai karaya ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Korar Fernandinho da Yaya Toure ta kara dagula wa City lissafi a karawarsu da CSKA Moscow

Kyaftin din Manchester City Vincent Kompany ya ce, yana da kwarin gwiwa za su yi nasara a gasar kofin Zakarun Turai duk da hadarin da suke ciki na sake ficewa da wuri.

City su ne na karshe a Group E bayan sun sha kashi 2-1 a gida, a hannun CSK Moscow.

Duk da wannan matsayi nasu Kompany na ganin kungiyar wadda aka korar mata 'yan wasa biyu a karawar ta ranar Laraba, za ta mike.

Kompany ya ce kowa zai iya bin ra'ayin ganin ba za mu kai labari ba, amma ni dai ina goyon bayan kowa a kungiyarmu kashi dari bisa dari na suya matsayinmu.

Wannan shi ne karo na hudu da kungiyar ke zuwa gasar Zakarun Turai, amma sau biyu tana kasa wuce matakin wasan rukuni, kuma ba ta taba wuce zagayen 'yan 16 ba.

Kyaftin din na City ya ce, ya kamata a sani cewa, su ba kungiya ce da ta yi shekara 20 tana zuwa gasar ba, saboda haka ba wai za ka tashi lokaci daya ba ne ka kai ga daukar kofin.

A wasanni hudu na rukunin na Group E, Bayern Munich tana da maki 12, As Roma tana da maki hudu, sai CSKA Moscow da maki hudu ita ma, Man City kuwa na da maki biyu.

Sauran wasannin da za a yi ranar Talata 25 ga watan Nuwamba; CSKA Moscow da AS Roma, Man City da Bayern Munich.

Ranar Laraba, 10 ga watan Disamba kuwa, Bayern Munich da CSKA Moscow, AS Roma da Man City.

Karin bayani