An sallami Nadal daga asibiti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rafael Nadal ya dauki kofunan manyan gasa 14 na duniya

An sallami Rafael Nadal dan wasa na uku a jerin gwanayen tennis na duniya daga asibiti kwana biyu bayan an cire masa kaban ciki.

A ranar 24 ga watan Oktoba Nadal dan kasar Spain mai shekaru 28 ya bayar da tabbacin cewa ba zai sake wasa ba a cikin wannan shekarar ta 2014 saboda yana bukatar a yi masa tiyata( ta appendix).

Nadal ba zai halarci gasar ATP World Tour ba, wadda za a fara ranar Lahadi a London.

Amma yana sa ran dawowa fagen wasa a lokacin gasar tennis ta duniya da za a yi a Abu Dhabi daga 1 zuwa 3 ga watan Janairu.