Manchester United ta doke Palace da ci 1-0

Manchester United Crystal Palace Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta matsa zuwa mataki na shida a teburin Premier

Manchester United ta samu nasara akan Crystal Palace da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 11 da suka buga a Old Trafford ranar Asabar.

A fafatawar mintuna 45 kafin a tafi hutu, babu wasu hare hare masu zafi da kungiyoyin suka kai wa juna, in banda wacce Fraizer Campbell ya buga ta haura tirke, da wadda Luke Shaw ya kai hari a raga.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Louis van Gaal ya saka Mata, kuma shigarsa filin ta yi amfani a inda ya ci kwallo daga tazarar yadi na 20.

Nasarar da United ta samu ya sa ta dare mataki na shida da maki 16, bayan buga wasanni 11, za kuma ta ziyarci Arsenal a Emirates a wasan mako na 12.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Liverpool 1 - 2 Chelsea

Burnley 1 - 0 Hull

Man Utd 1 - 0 Crystal Palace

Southampton 2 - 0 Leicester

West Ham 0 - 0 Aston Villa