Ghana ta amince ta dauki Avrant Grant koci

Avram Grant
Image caption Gram tsohon kocin West Ham da Ghana zai jagoranci horar da Ghana

Ghana ta ce ta zabi daukar Avram Grant a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafar kasar domin maye gurbin Kwesi Appiah.

Shugana hukumar kwallon kafar Ghana Kwesi Nyantakyi ya ce sun zabi Grant ne daga cikin masu horar da tamaula biyar da suka tattauna da su.

Idan har Grant ya amince da kunshin yarjejeniyar kwantiragin horar da Ghana, to zai jagoranci kasar buga wasan neman tikitin shiga gasar kofin Afirka da Uganda ranar 15 ga watan Nuwamba da fafatawa da za suyi da Togo ranar 19 ga watan Nuwamba.

Grant ya horar a Chelsea da West Ham da Portsmouth da Partizan Belgrade da kuma BEC Tero Sasana ta Bangkok inda ya rike mukamin daraktan tsare-tsare.

Ghana ta raba gari da kocinta Appaiah ranar 12 ga watan Satumba, bayan kammala gasar cin kofin duniya a Brazil, wanda kasar ta kasa kai wa wasan zagaye na biyu.