AFCON 2015: CAF za ta zauna don cimma matsaya

Caf Logo
Image caption Gasar kwallon kafar Afirka ta gamu da koma baya sakamakon cutar Ebola

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, za ta zauna domin fitar da matsaya kan kasar da za ta karbi bakuncin gasar kofin Nahiyar Afirka, ko kuma a dage gasar.

Morocco ta sake jaddada wa CAF cewar a dage gasar da ya kamata a buga a badi zuwa 2016 ranar Asabar a lokacin da wa'adin da hukumar ta bai wa kasar ta sanar mata da matsayarta.

Tun farko Morocco ta bukaci CAF ta dage gasar cin kofin Nahiyar Afirka da aka shirya gudanarwa daga watan Janairun badi, saboda tsoron kamuwa da cutar Ebola.

Kwamitin amintattu na CAF na fuskantar tsaka mai wuya, a inda har yanzu ba su sami kasar da za ta maye gurbin Morocco ba, duk da tayin da ta yi wa Masar da Nigeria da Algeria.

Idan har Morocco ta nace sai dai a daga gasar, ya zamo wajibi ga CAF ta samo kasar da za ta karbi bakuncin wasannin ko kuma a dage babbar gasar kwallon kafar Afikan zuwa wani lokacin.