Tarihin dan kwallon Algeria Yacine Brahimi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yacine Brahimi ya haskaka a gasar cin kofin duniya

A kowacce shekara sai manyan kungiyoyin Faransa sun yi layin daukar 'yan wasa daga makarantar horon 'yan kwallo kafa ta Clairefontaine idan sun yi bikin yaye dalibai.

A shekarar 2006 ne Yacine Brahimi ya kammala makarantar, inda Paris Saint-Germain ta yi kokarin daukar dan kwallon.

Sai dai iyayensa sunfi kaunar ya rattaba kwantiragi da Stade Rennais saboda kungiyar tana da tsarin karatun kasa da kasa da zai iya samun digirin digirgir.

Haka kuma shima dan wasan baya son ya yi wasa da karatunsa, saboda haka ya gwammace ya koma Stade Rennais da buga tamaula.

Sai dai komawa kulob din bai zo masa cikin sauki ba, domin ban da fama da jinyar rauni da ya dinga yi, sun kuma samu sabani tsakaninsa da koci Frederic Antonetti.

Nan danan sai ga dama ta samu na komawa taka leda da Granada ta Spaniya, inda suka amince da shi, suka kuma karbe shi hannu bibiyu, abinda ya rasa a baya.

Komawa Spaniya buga tamaula ya taimakawa Brahimi ta yadda ya fito da kwarewarsa ta yadda yake taka salon kwallonsa.

Idan ana son aga bajintar dan wasa ta asaka shi buga kwallo tsakankanin masu buga wasan tsakiya da kuma masu zura kwallo a raga.

Ya kware wajen lailaya leda da kwatota daga hannun abokan karawa da muka bai wa abokan wasa kwallon da za su zura a raga.

Sai dai wani fanni da Brahimi yake shan suka a Granada shine na rashin iya zura kwallo a raga.

Daga cikin wasannin 60 da ya buga, da kyar ya zura kwallaye uku ya kuma bayar da kwallaye biyar da aka zura a raga.

Haka kuma hazakar da dan kwallon ya nuna a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci a 2014, da ya wakilci Algeria ne ya bashi damar komawa Porto ta Portugal da buga kwallo.

Wannan damar da ya samu yasa Brahimi ya zura kwallaye biyu da bayar da kwallo daya da aka zura a raga a wasanni hudu da ya samarwa da Algeria tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka a badi.

Brahima ya karawa kansa martaba da kima a wasannin da yake buga wa Granada, yayin da yake ta kokarin bunkasa zura kwallaye kwallaye da kulob din.

A yanzu damar ta rage wa dan wasan Porto mai buga lamba takwasa.