Oscar ya tsawaita kwantiraginsa da Chelsea

Oscar Chelsea Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya ce yana jin dadi taka leda a Chelsea

Dan kwallon Brazil mai wasan tsakiya Oscar ya tsawaita kwantiraginsa da Chelsea domin ci gaba da buga tamaula a Stamford Bridge har zuwa 2019.

Mai shekaru 23, Oscar ya koma Chelsea ne daga Internacional ta Brazil a 2012 kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyar, ya kuma taimaka wa kulob din lashe Europa League a kakar farko da ya fara taka leda a Ingila.

Dan wasan ya ce "Ina jin dadin buga tamaula a Chelsea tsawon shekaru biyu da na yi, yanzu kuma ina da ragowar shekaru biyar da zan ci gaba da wasa".

Oscar, wanda ya buga wa kasarsa Gasar cin Kofin Duniya, ya buga wa Chelsea wasanni 92, inda ya zura kwallaye 27 a raga.