Tottenham na tsoron wasa a gida — Adebayor

Emmanuel Adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham da kocinta Pochetino na shan matsi a bana

Halin rashin dattako da magoya bayan Tottenham ke nunawa a White Hart Lane na kashe karsashin 'yan wasa inji Emmanuel Adebayor.

Magoya bayan kulob din sun yi ta yi wa 'yan wasan kuwwa a karawar da Stoke ta doke su 2-1 a gasar Premier, Tottenham din ta kuma yi rashin nasara a wasanni hudu daga cikin karawa shida da ta buga a gida a bana.

Adebayor ya ce "Mun fi kaunar mu buga wasa a waje, saboda ba ma samun karfin gwiwa daga magoya bayan mu".

Tottenham, wadda Newcastle ta doke a baya a gida, ta hada maki shida daga wasanni shida da ta buga a filinta.